Please Wait....
Close

  Kungiyar Kwadago Ta Goyi Bayan Yajin Aikin NASU, SSANU Da NAAT A Jami’o’i  Kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ta goyi bayan yajin aikin da ma’aikatan Jami’o’i na kasarnan ke yi, tana mai cewa, yajin aikin ya ci gaba, har sai an yi masu adalci.

  Shugaban kungiyar na kasa, Kwamred Ayuba Wabba, ne ya fadi hakan a wajen taron gangamin hadin kai a tsakanin kungiyoyin na, NASU, SSANU, da NAAT, wadanda suka yi wani taro na musamman a harabar ma’aikatar ilimi ta kasa da kuma harabar Majalisun tarayya, domin kara janyo hankulan Majalisun, Shugaba Buhari, da kuma al’umma kan abin da ke faruwa a Jami’o’in namu.

  Kwamred Wabba, ya ce, yin gangamin ya zama tilas, domin gwamnati ta ci gaba da saba alkawurran da aka yi da ita. Ya kara da cewa, yajin aikin zai ci gaba, har sai gwamnati ta yi abin da ya dace.

  Wabba ya ce, “Gangamin ya zama tilas ne, domin gwamnati ta ci gaba da saba alkawurranta. Don haka tilas ne yajin aikin ya ci gaba, har sai an yi abin da ya dace, domin kuwa sashen na ilimi yana kara tabarbarewa ne.

  < amp-ad>

  “Ya wajaba a yi duk abin da ya dace wajen farfado da wannan sashen, ko domin zuriyarmu ta gaba. Don haka tilas ne ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su mayar da hankulansu a kan wannan sashen. Dole ne mu tabbatar da an yi abin da ya dace.

  Shugaban kwamitin hadin gwiwan, kuma shugaban kungiyar, SSANU, Samson Ugwoke, ya bayyana dalilansu na kiran gangamin, inda kuma ya yi karin haske kan dalilansu na shiga yajin aikin, a lokacin da wakilan Shugaban Majalisar Dattawa suka tarbe su a Majalisar.

  Ugwoke, ya ce, “Muna son Majalisar kasa ta san dalilin nu na bacin ranmu, muna son su san su, su kuma magance su, a bisa rashin gaskiya da adalcin da ke faruwa a tsarin Jami’o’in kasarnan.

  Muna son su fa san halin da tsarin Jami’o’in kasarnan ke ciki.

  < amp-ad>

  “Muna son Majalisa ta zo Jami’o’inmu ta binciki dalilin da ya sanya dalibanmu da suka sauke karatu ba sa samun aiki. Mu fa ba ma jin dadin yanda abubuwa suke, muna kuma da tabbacin matukar ku ka sanya baki, duk dalilan da suka sanya mu shiga yajin aikin nan za a magance su.

  “Muna son mu janyo hankalin Shugaba, a kan wannan yajin aiki da muke yi, a bisa bukatarmu ta a aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2009.”

  Ya kuma yi nu ni da cewa, Kungiyoyin na su uku, sun sha yin taruka da gwamnatin tarayya, ba tare da wata nasara ba.

  “Manyan bukatunmu su ne, a maido da ‘ya’yan kungiyoyinmu da aka sallama a makarantun ‘ya’yan ma’aikata, wadanda kuma aka cire su daga tsarin biyan albashi na Jami’o’in, wanda kuma tuni, Kotu ta yi na’am da bukatarmu a kan hakan.

  < amp-ad>

  “Na biyu, batun biyan alawus dinmu, wanda tuni gwamnati ta ware Naira bilyan 23 a watan Satumba na shekarar 2017, wanda wasu jami’an gwamnati suka canza masu fasali zuwa ga wata kungiyar ‘yar’uwarmu, inda suka bar mana kashi 11 na kudin kacal.

  “Na uku, batun ragewa ‘ya’yan kungiyarmu albashi, inda sama da shekara kenan, wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar namu ba sa samun cikakken albashinsu. Na hudu, batun yin karin girma ga masu sana’ar hannu na matakan, CONTISS 14 da kuma 15, a bisa yarjejeniyar da muka cimma a baya da hukumar NAAT.”

  “Na biyar, darewa kan mukaman mu da kungiyar malaman Jami’o’i, ta yi, na Shida, a magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa tsarin Jami’o’inmu katutu.

  “Muna kuma son mu bayyana cewa, sau biyu kenen muna sanya hannu a kan takardar fahimta da Ministan kwadago, amma dai ba abin da aka yi. Ba kuma wani shiri na gaske a kasa, sai dai alkawurran baka kawai.

  < amp-ad>

  Sanata Bukar Abba Ibrahim, wanda shi ne ya wakilci Shugaban Majalisar ta Dattawa, ya tabbatar masu da cewa, Majalisar za ta yi duk abin da take iyawa wajen yakar cin hanci da rashawa a Jami’o’in.

  “Ina kuma tabbatar maku da cewa, kowane ma’aikaci sai ya sami dukkanin hakkinsa, da ma sauran bukatun naku da ku ka zo mana da su.

  Shi ma Sanata Shehu Sani, cewa ya yi, “Ina tabbatar maku, da sunan gwagwarmaya da kuma sunan al’ummar Nijeriya, zan yi duk abin da zan yi, wajen bin kadin bukatunku har karshe.”

  Shi kuwa Daraktan hukumar kula da manyan makarantu, a ma’aikatar Ilimin ta kasa, Mista Joel Ojo, cewa masu gangamin ya yi, Ma’aikatar Ilimin ta kasa, tana yin duk abin da ya dace wajen ganin an warware matsalolin da ke addaban Jami’o’in da gaggawa.

  < amp-ad>

  “Gwamnatin tarayya tana yin duk abin da ya dace. Don haka ina rokon ku da ku dan ba mu lokaci.


  Story Page