Please Wait....
Close

  Da dumi-dumi: Ministan kudi, Kemi Adeosun tayi murabus


  Adeosun resigns as Buhari's minister following NYSC scandal

  Ministan ta sauke ne yayin da take fuskantar matsin lamba kan zargin takardar karya na kammala aikin NYSC da ake zargin ta dayi.

  Rahotanni daga fadar shugaban kasa na tabbatar da cewa ministan kudi Kemi Adeosun tayi murabus daga majalisar gwamanatin tarayya.

  Ministan ta sauke ne yayin da take fuskantar matsin lamba kan zargin takardar karya na kammala aikin NYSC da ake zargin ta dayi.

  Wani majiya daga fadar shugaban kasa ya shaida mana cewa ministan ta mika takardar murabusa zuwa ofishin shugaban kasa kuma ana sa ran cewa nan bada jimawa zata fito fili tayi karin bayani game da matakin da ta dauka.

  Zargin da ake ma Kemi Adeosun

  A wata rahoto na musamman da jaridar Premium Times ta fitar, an gano cewa ministan ta mika takardar karya na NYSC bayan bata samu damar shiga cikin tawagar matasa da zasu gudanar da hidimar kasa dole.

  Rahoton dai ya jawo cece-kuce a fadin kasa inda wasu ke zargin shugaban kasa da cigaba da aiki da wacce ta saba ma dokar kasa.

  Dul da korafe-korafe da kafafen watsa labarai da yuan Nijeriya keyi game da lamari ministan bata fito fili tayi bayani game da zargin da ake mata.

  Hakazalika fadar shugaban kasa bata yi karin haske game da zargin.

   
  Story Page